Hedkwatar soji ta khatamul ambiya ta fitar da sanarwa mai karfi bayan da shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar fadada hare-hare kan iran a makon mai zuwa, inda zai hari kan muhimman wurare a kasar da suka shafi cibiyoyin wutar lantarki da kuma gadoji da mutane ke amfani da su
Kakakin dakarun sojin kasar iran laftanar kanar Ibrahim Zolfiqari yace idan sojojin Amurka suka kadddamar hari kan muhimman wurare na amfani jama’aa a kasar iran to ko shakka babu za ta mayar da martani kan muhimman wurare dake fadin yankin baki daya, kuma ya soki gwamnatin Amurka game da mataken da take ci gaba da dauka na yunkurin rusa yankin yammacin Asiya
Haka zalika ya kara da cewa iran ba za ta taba bari Amurka ta kafa wani sansani na daban ba a yankin da zai rika tsoma baki kan mashigar Hurmuz wanda kasar iran ta sanya shi a matsayin jan layi
A wani bangare kuma dakarun kare juyin musulunci na iran sun sanar a yau Alhamis cewa dakarunsu sun kaddamar da mummunan hari kan sansanin sojin Amurka dake shaik Isa na kasar Baharain, harin ya rusa dukkan kayyakin da naurorin rada da cibiyoyin dake ba wa jirgen yaki makiya mai,
Yace wannan harin mayar da martani kan hare-haren da sojojin Amurka masu kashe yara kanana suka kai ta sama a sansanin soji dake bakin teku da sauran wuraren da ba na soja ba, da suka hada da wani Asibitin masu cutar kansa na yara da kuma wata cibiyar samar da ruwa ga masu zuwa ziyara Karbala a iraki a yankunan dake kan iyaka,