Malaman da suke halattan taron hadin kan al-ummar musulmu ko kuma makon hadin kai a nan Tehran sun ci gaba da ayyukansu a safiyar yau Jumma’a. Inda malamai da dama suka gabatar da jawabai masu muhimmanci.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban kungiyar ‘majalisar malaman muhammadi’ Sheikh Abdulkadir Alousi yana cewa: Manufar wannan taron itace tattauna dukkan al-amura da suka shafi al-ummar musulmi. Muna iya amfani da wannan damar don tattauna batun ayyukan hajji. Ya kuma kara da cewa: wannan taron dama ce ta tattauna batun hadin kai a tsakanin al-ummar musulmi ga malamai wadanda suke da wannan ra’ayin. Kuma dole ne muyi kokarin haduwa da manya manyan malaman addini.
Sheilh Alousi ya kamala da cewa: Mun rika mun bayyana goyon bayammu ga Falasdinu da Gaza, da kuma Lebanon da Yemen.
Sai kuma Sheikh Mohammad Al-asi daga kasar Amurka, wanda ya kasance mamba a ‘majalisar koli ta hadin kan addinai ta duniya’ wanda yake cewa ‘duk tare da mummunan halin da Musulmi suke ciki a duniya muna iya bude sabon shafi wanda zai hada kan al-ummar musulmi. Abinda yake faruwa a kasar Falasdinu ya ishe mu hujja ta samar da hadin kai a tsakanimmu.