Iran Tana Daga Cikin Kasashe 3 A Nahiyar Asiya Wadanda Suke Da Lamunin Samun Isasshen Abinci

Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa kasar a halin ayanzu tana daga cikin kasashe uku na gaba a kan abinda ya shafi

Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa kasar a halin ayanzu tana daga cikin kasashe uku na gaba a kan abinda ya shafi samun isasshen abinci mai lafiya da kuma wadatacce a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan kiwon lafiya Muhammad Reza Zafarkandi yana fadar haka a jiya litinin a taron raya ranar abinci da duniya wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar gidajen radio da talabijin a nan birnin Tehran.

Ministan ya kara da cewa, samun abinci mai gina jiki da kuma bada sinadaran da jiki yake bukata yana daga cikin abubuwan da suke bada lafiya ga jiki.

Har’ila yau wannan yana kwantar da hankalin mutanen ko wace kasa wacce take da wannan matsayin na samar da abinci da kuma lamunin lafiyar abincin.

Ministan ya ce akwai kamfanonin samar da abinci a cikin kasar kimani 17,000 wadanda ma’aikatar take kula da dukkan abincin da suke samarwa, don tabbatar da lafiyansu da kuma ingancinsu kafin su sayarwa mutane.

Sannan ma’aikatar tana da dakunan bincike har 450 wadanda suke gwada lafiyar abincin da wadannan kamfanoni suke samarwa a duk fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments