Iran Tace: Amurka Bata Da Hakkin Tsara Mana Yadda Zamu Tafiyar Da Kasar Mu

Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya

Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X.

Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi.

Ministan ya kara da cewa, ya maida martani da cewa: Amurka ce da alhakin marawa ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa a duniya, kuma gwamnatin shugaban Biden kadai ta kashe dalar Amurka biliyon 23 don kissan Falasdinawa kimani 60000 a Gaza. Don haka yana kira ga Amurka ta dakatar da tallafin da take bawa HKI wacce mafi yawan kasashen duniya ta dauketa a matsayin yar ta’adda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments