Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’il baqae yayi tir da harin da HKI ta kai a kudancin labanon kuma ta bayyana hakan a matsayin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’il baqae yayi tir da harin da HKI ta kai a kudancin labanon kuma ta bayyana hakan a matsayin keta hurumin kasar , yace kasashen Amurka da faransa a matsayinsu na garanto wajen dakatar da bude wuta suke da alhakin taka mata burki kan hare-haren da take kaiwa.

Wannan harin da Isra’iala ta kai a kudancin labanon rahotanni sun nuna cewa shi ne kusan karo na 5000 da ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma  tsakaninsu.

Kuma wanann ba shi ne karon farko da Isra’ila ke keta yarjejeniyar da aka cimma ba, saboda  akwai dalilai masu yawa da suka tabbatar da haka saboda ta saba yi a yankin gaza da ma labanon din tun a baya,

Ci gaba da keta yarjejeniyar da HKI ke yi na kai hare hare a kasar labanon yana shafar fararen hula sosai, kuma yana lallata muhimman gine-gine. Kuma yana kawo ci kasa a ayyukan raya kasa da kuma tattalin arzikin kasar,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments