Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yi maraba da tsayar da wuce gona da irin HKI akan kasar Lebanon.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i, ya ce, jamhuriyar musulunci ta Iran tana nuna goyon bayanta ga gwamnati da kuma gwagwarmayar al’ummar Lebanon.
Har ila yau kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i, ya kuma jaddada cewa a kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin kira da a kawo karshen laifukan yaki da wuce gona da irin da HKI take yi, bisa cikakken goyon bayan Amurka da wasu kasashen turai.
Baka’i ya kuma kara da cewa, bayan shudewar watanni 14 daga fara yakin kare dangi da kisan kiyashi, da kuma sammacin da kotun kasa da kasa ta manyan laifuka ta fitar na kamo shugabannin ‘yan sahayoniya, ra’ayin mutanen duniya ya sauya akan HKI.
Yanzu abinda duniya take jira shi ne ganin an kamo Natenyahu da Yoav Gallant domin tsayar da su a gaban wannan kotu ta duniya su fuskanci sharia.
Har ila yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce, nauyi ne da ya rataya a wuyan duniya su yi matsin lamba akan ‘yan sahayoniyar su tsaida yaki, domin samar da tsaro da sulhu a yammacin Asiya.