Iran ta yi maraba da hukuncin kotun faransa na yi wa Esfandiari saki bisa sharadi  

Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa

Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi.

‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza .

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce Tehran za ta ci gaba da bin diddigin shari’ar Esfandiari, ‘yar kasar wacce malamar jami’a ce mai shekaru 39 da ke zaune a Lyon, har sai ta samu cikakken ‘yanci tare da komawa gida,” in ji Baghaei.

Esfandiari, wacce ta zauna a Faransa kusan shekaru takwas, an cafke ta ne a asirce a ranar 1 ga Maris, 2025, wanda ya sa danginta sanar da hukumomin Iran game da bacewarta.

Biyo bayan hakan ne binciken da ofishin jakadancin Iran ya nuna cewa ‘yan sandan Faransa ne suka kama ta.

An tsare Esfandiari ne sabdoa aika sakon a manhajar Telegram mai goyon bayan Falasdinu, bayan harin Hamas na 7 ga watan Oktoba 2023.

Kamen nata ya jawo kakkausar suka daga Jamhuriyar Musulunci.

Tehran ta ce hakan yana da nasaba da siyasa da kuma keta ‘yancin fadin albarkacin baki.

A ranar Talata, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Vahid Jalalzadeh ya ce an gabatar da sunan Esfandiari a wani shirin musayar fursunoni da Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted