Iran ta yi kira ga kungiyar Shanghai ta yi Allah wadai da barazanar Trump

Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya

Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar.

A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari.

Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta  dokokin kasa da kasa, da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya haramta amfani da karfi karara a kan iyakokin kasa da ‘yancin kai.

Takht Ravanchi ya bayyana cewa Iran ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da wannan hali da ba za a amince da shi ba tare da daukar matakan da suka dace don kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.

Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya sake jaddada matsayar kasar Iran da cewa duk wani yunkuri daga Amurka zai fuskanci mai da martani cikin gaggawa.

Ya yi kira da a fitar da sanarwar hadin gwiwa ta SCO da ke yin Allah wadai da barazanar Amurka tare da yin kira ga kwamitin sulhun da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments