Iran ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka bisa tsarin yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar
A yayin bikin karo na 62 na kafuwar kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin Tehran, ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar Iran na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka, musamman ta hanyar yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).
A cikin jawabin da ya yi ga jakadun kasashen Afirka a Iran, Araghchi ya yaba da dabi’u da tarihin gwagwarmayar al’ummar Afirka, yana mai cewa Afirka, mai al’umma biliyan 1.4, na zaman kawa a huldar tattalin arziki ga Iran.
Ya kara da cewa: “Iran da kasashen Afirka za su iya hada kai da juna saboda irin karfin da suke da shi: dimbin albarkatun kasa a bangaren Afirka da fasahohin zamani a bangaren Iran.”
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma tunatar da zurfafa alaka ta tarihi da ke tsakanin Iran da nahiyar Afirka, inda ya yi kira da a fadada hadin gwiwa a fannoni daban-daban: masana’antu, noma, kiwon lafiya, ilimi, makamashi, yawon bude ido, da ababen more rayuwa.
Ya yi maraba da nasarar taron koli na hadin gwiwar tattalin arziki na Iran da Afirka karo na uku da aka gudanar kwanan nan a birnin Tehran, yana mai kallon hakan a matsayin wata alama mai kyau ga makomar dangantakar bangarorin biyu.
A karshe Araghchi ya tabbatar da cewa Iran za ta tsaya kafada da kafada da nahiyar Afirka a kokarinta na samun ci gaba.