Search
Close this search box.

Iran Ta Yi Gargadi Game Da Ha’incin Amurka Da Isra’ila A Tattuanwar Tsagaita Wuta

Kasashen Iran da na Qatar sun tattauna game da makomar tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Iran ta yi gargadi game da “ha’inci da rashin

Kasashen Iran da na Qatar sun tattauna game da makomar tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Iran ta yi gargadi game da “ha’inci da rashin gaskiya” na gwamnatin Isra’ila da babbar mai goyon bayanta, Amurka.

Ministan harkokin wajen Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ne ya yi wannan gargadi a wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ranar Juma’a.

Tattaunawar tasu ita ce ta biyu cikin sa’o’i 24.

M. Kani ya ce Amurka na ba da makamai ga Isra’ila wanda hakan ya sa ta zama “mai bangare a rikicin, ba mai shiga tsakani ba.”

Don hake na ke matsa kaimi akan a yi amfani da duk hanyoyin da suka dace domin tilasta wa Isra’ila kawo karshen kisan gilla da kashe kashen da take aikatwa a Gaza, inji ministan harkokin wajen kasar ta Iran.

Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen kasar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya ce tattaunawar shiga tsakani don aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza ta cimma mataki mai muhimmanci.

Duk da tattaunawar tsagaita bude wuta da ake yi, gwamnatin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

Adadin Falasdinawa da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila ya zarce  40,000 tare da jikkata wasu fiye da 92,400, a yayin da yakin ya shiga watansa na goma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments