Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Manufar HKI akan Syria a fili take ba a boye ba.”
Baka’i ya ci gaba da cewa; Manufar HKI ita ce rusa duk wani karfi da Syria take da shi na yaki, da kuma lalata tattalin arzikinta, domin share fagen shimfida iko a kasar da kuma a cikin wannan yankin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya kuma ci gaba da cewa; matsayin jamhuriyar musulunci ta Iran akan kasar Syria, a fili yake wanda shi ne kare hadin kan wannan kasa da hana ta tarwatsewa da kare daukakarta a matsayinta na kasa mai ‘yanci da kuma al’umma mai tsawo tarihi na ci gaba,sannan kuma mai tasiri a cikin wannan yanki na yammacin Asiya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya dora alhakin abinda yake faruwa a Syria, akan dukkanin wadanda su ka taka rawa wajen jefa kasar cikin halin da take a yanzu.
Wuraren da HKI ta kai wa hare-hare a daren jiya sun hada da sansanin sojan runduna ta 47 da sojoji Syria dake yankin Humah ta yamma, haka nan kuma rumbun ajiyar makamai na sojan sama a kusa da garin shahdaha, da ya jikkata mutane 4,kamar yadda kamfanin dillancin labaurn “SANA” na kasar ta Syria ya nakalto.
A birnin Damascuss ma sojojin HKI sun kai wasu hare-haren da su ka hada da kusa da fadar shugaban kasa. Kafafen watsa labaru sun ambci shahadar mutum daya, da kuma jikkatar wasu.