Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Irin Isra’ila Kan Kudancin Kasar Lebanon

Kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin

Kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon. Ya jaddada cewa, sun biyo bayan yadda aka ci gaba da yin sassauci da rashin daukar nauyin masu daukar nauyin yarjejeniyar tsagaita bude wuta – Faransa da Amurka – yana mai nuni da alhakin kai tsaye da ke kan kasashen biyu a wannan fanni.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya dauki hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a jiya da rana da kuma dare kan wasu wurare a kudancin kasar Lebanon a matsayin cin zarafi ga yankin kasar Lebanon da kuma ikon mallakar kasa. Ya kuma bayyana kakkausar suka ga irin wadannan laifuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted