Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza

Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu.

A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da kashe-kashe da aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan da kuma muggan hare-haren da ake kai wa kan wurare masu tsarki na Musulunci a birnin Quds mai girma.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta kuma yaba da matakan da gwamnatoci da al’ummomi masu neman ‘yanci suka dauka wajen bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, tare da jaddada nauyin da ke wuyan kasashen duniya na dakatar da kisan kiyashi da kuma ba da taimako cikin gaggawa ga al’ummar Gaza da ake zalunta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted