Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya soki kasashen Faransa, Jamus da kuma Burtania da yadda suka yi dirar mikiya a kan shirin Nkliyar kasar Iran a cikin yan watannin da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Bghaei yana fadar haka a yau Litinin, a taron da yan jarida da ya saba gabatarwa a ko wace rana irin ta yau.
Baghaei ya zargi kasashen guda uku da amfani da tsarin SnapBack wanda ya zo cikin yarjeniyar JCPOA na shirin Nukliyar kasar Iran a inda baida dace ba. Ya kara da cewa kasashen sun yi amfani da Snapback kan kasar Iran ne don biyan bukatun Amurka na tursasawa gwamnatin JMI ta mika kai ga bukatun ta.
Banda haka ya ce sharuddan da kasashen uku suka shimfiyawa kasar don dakatar da amfani da snapback ma ba abin amincewa ne ga kasar Iran. Kuma ba wani mai hankali da zai amince da wadan nan sharuddan.
Daga karshe sai suka hada batun shirin nukliyar ta kasar Iran da tattaunawa da Amurka, wadanda basu hadu ba. Yace kofar diblomasiyya a bude take, amma kuma Iran ba zata saryar da hakkin na amfani da fasahar makamashin nukliya ba.
Daga karshe Baghaei ya bukaci ya bukaci kasashen duniya su yi watsi da takunkuman tattalin arzikin da aka sake dorawa Iran saboda Snapback.