Iran Ta Soki Takunkuman Kasashen Turai Kan Bangaren kamfanonin Sufirinta

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya soki kungiyar Tarayyar Turai kan matakin da ta dauka na sanyawa kamfanonin jiragen sama da na ruwa na kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya soki kungiyar Tarayyar Turai kan matakin da ta dauka na sanyawa kamfanonin jiragen sama da na ruwa na kasar takunkumi.

Da yake Allah wadai da matakin da EU ta dauka kan kamfanonin, Abbas Araghchi ya ce: Shugaba Zelensky da kansa ya tabbatar da cewa babu wani makami mai linzami na Iran da aka fitar zuwa Rasha.

Babban jami’in harkokin diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa: Yanzu haka kungiyar tarayyar turai tana shirin yin amfani da uzurin karya na fitar da makamai masu linzami zuwa kasar Rasha domin sanyawa kamfanonin jigilar kayayyaki takunkumi

Kungiyar Tarayyar Turai dai ta sanar da kakaba takunkumi kan layukan jiragen ruwa na Iran saboda ikirarin cewa tana da hannu wajen kai wa Rasha makamai a yayin yakin da ake yi a Ukraine.

Hukumar Tarayyar Turai, ta fada a ranar Litinin cewa, ta kakaba takunkumi kan layukan sufurin jiragen ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRISL), da darektanta Mohammad Reza Khabani, da wasu hukumomi da daidaikun mutane.

Matakin ya hana duk wani ciniki da su.

Tarayyar Turai ta yi ikirarin cewa mutane da kungiyoyin suna da hannu cikin jigilar jiragai marasa matuka na Iran (UAVs), makamai masu linzami, da fasahohi da sauran abubuwan da ke da alaka da hakan zuwa Rasha don amfani da su a yakin Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments