Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu.
A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan.
Tunda farko dama kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya.
A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara yayin wata hira da tashar 14 ta Isra’ila cewa “Saudiyya za ta iya kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, suna da kasa mai girma.”
Kungiyar ta OIC ta dauki wannan a matsayin tsokana ga Saudiyya, kuma cin zarafi ne ga ’yancin kai, tsaron kasa da kuma yankinta, da kuma keta dokokin kasa da kasa da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.