Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3

Gwamnatin kasar Iran  ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu

Gwamnatin kasar Iran  ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa .

Tsibiran guda 3 da ake takaddama akansu Abu musa da tunbu babba da karami  suna yankin tekun fasha ne tsakanin mailand na iran da kuma hadaddiyar daular larabawa, tsibbiran wani bangare ne na kasar iran tun karnoni da suka gabata da ke cike da abubuwa da suka safi doka da tarihi  a iran da kuma kasa da kasa.

Iran ta jaddada cewa dukkan wadannan tsibirai guda 3 wani bangare na kasarta da babu tantama akai,don  haka ta yi kira ga kasashen larabawa da su guji daukar duk wani mataki akai da zai iya cutar da dangantakar dake tsakaninsu.

A ranar 30 ga watan nuwambar shekara ta 1971 ne dakarun birtaniya suka janye daga tsibiran kuma kwana biyu kafin kafa hadaddiyar daular larabawa a hukumance aka dawo da ikon mallakar tsibiran ga kasar iran bisa doka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted