Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun yi musayar sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye.
Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece cewa, Muna cikin shiri da tanadin sake dawo da alaka da kasar Syria anan gaba.
Har ila yau. Shaibani ya ce; Muna bin diddigin abubuwan da suke faruwa a Syria, kuma za mu dauki matsaya a lokacin da ya dace.”
Haka nan kuma ya ce; Muna kallon Syria ne a matsayin kasa wacce take da matsayi a cikin yankin yammacin Asiya, kuma mun yi imani da cewa, al’ummar kasar ne za su ayyana makomarta, don haka ya zama wajibi dukkanin bangarorin siyasar da ake da su a kasar su shiga ayi da su.”
Dangane da ziyarar da ya kai kasar Rasha, Shaibani ya ce; yana yin ziyarar ne domin tattaunawa da jami’i mai kula da harkokin Syria da kuma mataimakin ministan harkokin waje.
Shaibani ya kuma kara da cewa; kasashen Iran da Rasha suna da mastaya iri daya akan batutuwa mabanbanta da su ka shafi Syria,kuma a yayin wannan ziyarar sun cimma matsaya akan ci gaba da tattaunawa da yin shawarwari a tsakaninsu.