Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare guda ta kasa da kasa wacce ba’a dade da samar da ita a farkon wannan shekarar.
Isma’el Baghaei ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Alhamis, inda yayi tir da Amurka wace ta fara fara dorawa JMI takunkuman tattalin arziki tun fiye da shekaru fiye da 40 da suka gabata. Kuma hakan take hakkin bil’adama.
Yace a farkon wannan shekarar ne dai babban zauren MDD ta samar da kuduri mai lamba 79/293 inda ta bayyana takunkuman tattalin arziki na bangaren guda ko kasar guda, baya bias ka’ida kuma duk kasar da ta yi haka tana take hakkin bil’adama a kan kasar da ta dorawa.
Majalis ta sanya ranar 4 gawatan Decemba na kowace shekara a matsayin ranar haramta takunkuman tattalin arziki na bangare guda. Wato MDD ce kadai take da alhakin dorawa wata kasa takunkuman tattalin arziki.
Yace takunkuman da gwamnatin kasar Amurka ta dorawa JMI tun farkon juyin juya halin musulunci har zuwa yanzu sun yisanadiyyar kashe mutane da dama a klasar Iran. Musamman takunkuman sayan maganin cututtukan masu tsanani.