Iran Ta Nuna Damuwarta Akan Tabarbarewar Harkokin Tsaro A Kasar Libya

A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki

A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini.

Dr. Baka’i ya yi ishara da nauyin da ya rataya a wuyan dukkanin wadanda suke da hannu a fadace-fadacen da suke faruwa a cikin babban birnin kasar ta Libya, sannan ya bukace su da su taimaka wajen dawo da zaman tsaro a cikin kasar.

Haka nan kuma ya bukace su da su koma kan teburin tattaunawa mai maimakon amfani da karfi, su kuma kaucewa bai wa kasashen waje damar tsoma baki a cikin harkokin cikin gidansu.

Dr. Baka’i, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda rikicin na kasar ta Libya ya rutsa da su, da kuma yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments