Kasar Iran ta baje kolin ci gaban da ta samu da kuma fasahar ilmin kimiyan da take da shi, a baje kolin kayakin ci gabanta a Jami’ar Damascus babban birnin kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu ana gudanar da baje kolin kayakin ci gaban da JMI ta samu a jami’ar ta Damascus, kuma mataimakin shugaban kasa kan al-amuran kimiya da fasaha na JMI ne tare da hadin kai da kungiyar daliban Jami’o’i a kasar Siriya ne suka shirya baje kolin.
Labarin ya kara da cewa daliban jami’o’in JMI 15 ne suke halattar baje kolin na kwanaki 5, wato daga ranar 9-13 ga watan Yunin da muke ciki.
Shugaban baje kolin, Zakizadeh ya bayyana cewa manufar wannan baje koli ita ce yada ci gaban da kasar Iran ta samu a wannan fagen ga kasashen makobta da kuma musulmi, Ya kara da cewa ya na fatan dukkan daliban Jami’o’in da suke halattar baje kolin zasu amfana da shi.
Ministan manya manyan makarantu na kasar Siriya wanda ya sami damar halattan baje kolin ya bayyana jin dadinsa da sanin irin yadda daliban jami’o’i a kasar Iran suka sami ci gaba, kuma suke yada shi zuwa ga sauran kasashen musulmi.