Majiyar gwamnatin kasar Iran a kasar Siriya ta bayyana cewa labarin kama sojojin kasar a lardin Hasaka na kasar Siriya ba gaskiya bane.
Kamfanin dillancin labaran ‘Sahab’ na kasar Iran ya nakalto wata majiya ta gwamnatin kasar Iran a Siriya na cewa wasu kafafen yada labaran HKI sun yada labarin cewa a hare haren na baya bayan nan, wadanda sojojin HKI suka kai a yankin Musayyaf na lardin Hasaka a tsakiyar kasar Siriya sun kama sojoji da dama daga ciki har da wasu sojojin kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa Iran bata da sojoji a kasar Siriya, ballanta a yankin Musayyab. Ta kuma kara da cewa sojojin kasar Siriyane a wajen, kuma a hare haren da HKI ta kai kan yankin ta kashe mutane 18 a yayinda wasu 37 suka ji rauni.
Hare haren dai su ne mafi muni wadanda sojojin HKI suka kai a baya bayan nana a kasar ta Siriya.