Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan

Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da

Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a birnin Al-Fashir na kasar Sudan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kira harin a matsayin ” keta dokokin jin kai na kasa da kasa.”

Ta kuma jaddada bukatar gaggauta dakatar da kai hare-hare kan fararen hula da muhimman ababen more rayuwa a kasar Sudan, tare da bayyana cewa dole ne a warware rikicin kasar ta hanyar “tattaunawa tsakanin ‘yan Sudan.”

Iran ta bayyana juyayinta ga wadanda lamarin ya ritsa dasu tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Sama da mutane 70 ne aka kashe a wani harin da aka kai da jirghi marar matuki da dakarun sa kai na (RSF) suka kai a wani masallaci da ke Al-Fashir a ranar Juma’a, in ji sojojin Sudan da masu aikin ceto a yankin.

lamarin na ranar Juma’a ya nuna wani sabon tashin hankali a yakin basasa na shekaru uku tsakanin sojojin Sudan da RSF.

Tun daga watan Afrilun 2023, yakin Sudan ya kashe dubunnan mutane tare da raba wasu miliyan 12 da muhallansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin a matsayin daya daga cikin mafi muni a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments