Iran Ta La’anci Hare-haren Isra’ila Kan Yemen

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke yi kan

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke yi kan ababen more rayuwa na kasar Yemen.

Ismail Baqai ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai ranar Alhamis kan cibiyoyin Yemen da suka hada da tashar samar da wutar lantarki ta Sanaa, da tankunan mai na Ras Al-Eisa, da tashar ruwan Hodeidah.

Ya bayyana wadannan hare-hare a matsayin cin zarafi da keta dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.

Jami’in diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa: Laifukan da yahudawan sahyoniya suke aikatawa suna faruwa ne tare da goyon bayan Amurka, kuma Washington tana da hannu a cikin take hakki da laifukan da gungun masu laifi da ke mulkin Tel Aviv ke aikatawa inji shi. »

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yaba da irin goyon baya da hadin kai da al’ummar kasar Yemen suke bai wa al’ummar Palastinu da ake zalunta, inda ya ce al’ummar duniya da kuma al’ummar musulmi suna da alhakin da ya rataya a wuyansu na shari’a wajen kawo karshen zaluncin gwamnatin sahyoniyawa da kuma hukunta wannan gwamnatin kamar yadda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta bukata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments