Iran ta bayyana anniyarta ta yin hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran “na maida hankali” wajen hada kai da hukumar ta IAEA.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Gharibabadi ya yaba da tattaunawa mai ma’ana” da ya yi da Rafael Grossi, shugaban IAEA, a hedkwatar IAEA a Vienna.
Ya ce, bangarorin biyu sun tattauna batun hadin gwiwa tsakanin da warware batutuwan da ake takkadama, da batun tsaron cibiyoyin nukiliya, da sabbin batutuwan da suka shafi nukiliyar iran, da kuma dage takunkumi.
Jami’in na Iran ya kara da cewa dadadden hadin gwiwar dake tsakanin Iran da hukumar ta IAEA ya ba su damar warware ‘yan kadan daga cikin batutuwan da suke rage bambance-bambancen dake akwai.