Iran Ta Kudiri Anniyar Karfafa Alakarta Da Kasashen Afirka

Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike

Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar.

A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref da jakadun kasashen Afirka a Tehran.

Baghaei ya bayyana cewa, taron ya nuna aniyar Iran na karfafa alaka da fadada hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban-daban na moriyar juna.

A yayin ganawar, Aref ya bayyana cewa, dabarun gwamnatin Iran, karkashin shugaba Masoud Pezeshkian, ya yi daidai da ainihin manufofin Iran na inganta alaka da kasashen Afirka.

Ya jaddada manufar karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, a bangarori da dama, da kuma shiyya-shiyya.

“Idan aka yi la’akari da irin karfin da muke da shi, ta hanyar hada kai da hada albarkatunmu, za mu iya ba da gudummawa sosai ga ci gaban dangantaka da kuma yi wa jama’armu hidima,” in ji Aref.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments