Iran Ta Kori Jakadan Australia Daga Tehran, Don Maida Martani

Gwamnatin kasar Iran ta sallami jakadan kasar Autralia daga Tehran bayan da gwamnatin Australia ta yi haka ba tare da wani dalili amintacce ba. In

Gwamnatin kasar Iran ta sallami jakadan kasar Autralia daga Tehran bayan da gwamnatin Australia ta yi haka ba tare da wani dalili amintacce ba. In banda mummunan siyasar Canberra da nuna kiyayya ga JMI.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esma’ek Baka’ei yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa korar da gwamnatin Australia yayiwa jakadan Iran a Canberra bai dace ba kuma ya sabawa dukkan ka’idojin diblomasiyya. Don haka ne Tehran taga yakamata ta yi hakan don maida martani mai kama da nata.

Baqaei ya kara da cewa irin wadan nan matakan ba zasu taimakawa kowa ba, sai kara tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Ya kuma kammala da cewa, bisa dokokin diblomasiyya Iran ta rage darajar diblomasiyya tsakanin Canberra da Tehran, don haka ta sallami jakada Australia daga Tehran, sai dai duk tare da hakan karamin ofishin jakadancin kasar Iran a birnin Canberra na ayyukan khidimawa Iraniyawa da suke cikin kasar.

Daga karshen Tehran ta musanta tuhumar kan cewa tana kin yahudawa, abinda ya tada rigimat tun farko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted