Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta kaddamar da kayakin aikin da ake bukata don samar da garin sinadarin (Tellurium Dioxide) wanda ake hada maganin cutar daji wanda ake kira (Iodine-131) da shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar makamashin nukliyar ta Iran, na cewa ana samar da wannan sinadarin ne tare da amfani da makamashin nukliya. Kuma a halin yanzu kasar Iran zata iya samar da maganin wanna cutar a cikin gida.
Labarin ya kara da cewa, idan JMI ta fara samar da maganin, zata bar dogaro da kasashen wajen don magance cutar a cikin gida, sannan wata dama ce ta samun kudaden shiga daga kasashen waje.
Don haka a halin yanzu Iran tana da damar samar da maganin cutar mai suna Iodine-131 a cikin gida. Kafin haka dai kasashe kadan ne suke da fasahar samar da wannan maganin a duniya, kuma da tsada.