Iran Ta Jaddada Bukatar Kasar Falasdinu Ta Zama Cikekken Mamba A MDD

Jakadan kasar Iran a MDD ta jaddada bukatar kasar Falasdinu ta zama mamba a MDD a matsayin kasa mai cikekken yencin kai kamar sauran kasashen

Jakadan kasar Iran a MDD ta jaddada bukatar kasar Falasdinu ta zama mamba a MDD a matsayin kasa mai cikekken yencin kai kamar sauran kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta nakalto Amir Saeed Iranwani yana fadar haka a taron babban zauren MDD don tattauna batun hawa kan kujerar VETO wanda gwamnatin Amurka tayi a taron kwamitin tsaro tare da bukatar kasar Falasdinu ta zama mamba na din din din a majalisar.

Iranawani, a jawabin da ya gabatar a taron ya jaddada bukatar kasar Falasdinu ta zama cikekken mamba a majalisar, ya kuma kara da cewa hawa kan kujerar VETO wanda gwamnatin Amurka ta yi a taron ya sabawa bukatar mafi yawan kasashen duniya. Jakadan ya kara da cewa JMI da mafi yawan kasashen duniya suna ganin hanya guda ta warware matsalar al-ummar Falasdinu ita ce bawa falasdinawa damar fayyace makomar kasarsu, da kuma basu cikken matsayi na yentacceyar kasa a MDD.

Bayan fara yaki a gaza a cikin watan Octoban shekarar da ta gaba ne kasashen duniya suka fara matsin lamba don tabbatar da cewa an bawa kasar Falasdinu cikekken mamba a MDD. Amma a ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata, mabobi 12 cikin 15 a kwamitin tsarin MDD daga ciki har da kasashen Rasha da Chaina sun amince da kudurin amma Amurka ita kadai ta hau kan kujerar VETO inda ta hana kudurin wucewa ko kuma amincewar majalisar. Ya zuwa yanzu dai kasashen duniya 140 cikin 193 sun amince da kasar Falasdinu a matsayin cikekken kasa, amma Amurka ta hana ta zama cekekken maba a MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments