Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Mayar Da Martani Kan Bakar Siyasar Kwamitin Gwamnonin Hukumar IAEA

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Zata mayar da martani mai gauni kan yadda ake siyasantar da batun nukiliya a cikin kwamitin gwamnonin cibiyar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Zata mayar da martani mai gauni kan yadda ake siyasantar da batun nukiliya a cikin kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya jaddada cewa: Idan aka mayar da batun Iran na nukiliya siyasa a taron kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA, bai kamata daya bangaren ya sa ran Iran za ta ci gaba da yin aiki da cikakken kamun kai ba tare da mayar da martani ba. Maimakon haka, Iran za ta gudanar da mu’amalarta da siyasarta daidai da halayensu da manufofinsu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta gidan talabijin na Iran a yammacin jiya Talata, dangane da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan rahoton baya-bayan nan da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafa’el Grossi ya gabatar, wanda ya haifar da cece-kuce game da wani kuduri mai tsauri kan Iran a taron kwamitin gwamnonin da za a yi a mako mai zuwa, Gharibabadi ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran mamba ce ta yarjejeniyar hana kera makamin nukiliya da yaduwarta, kuma tana yin riko da dokokin da yarjejeniyar ta cimma tare da karewa.

Ya kara da cewa: “Iran ta aiwatar da alkawuran da ta dauka tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyarta. Ko da yake ya kamata hukumar ta IAEA ta kasance kungiya ce ta fasaha da doka, amma ra’ayoyin siyasa suna yin tasiri kanta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments