Ana taro kan yadda manzon Allah mohammad dan Abdullahi (a) ya zauna da wadanda ba musulmi ba a rayuwarsa a Madina.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto hukuma mai kula da al-adu da kuma al-amuran addinin Musulunci a nan Iran tana cewa ana gudanar da wannan taron ne a dai dai lokacinda aka fara bukukuwan cika shekaru 1500 na hijirar manzon Allah (s).
Labarin ya kara da cewa an sabi baki wadanda suka gabatar da jawabi masu muhimmanci daga kasashen Iran, Lebanon da kuma Masar.
Ahmad Mobaleghi na mamba a kwamitin al-amuran addini na hukumar ya kawo ayoyin al-kur’ani wadanda suka yi mgana kan yadda manzon Allah yayi mu’amala da yahudawan da ya samu a Madina, kuma ya ce wadannan ayoyi kekyawar misali ne nazamantakewar Musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Louis Saliba wani marubu ce kirista daga kasar Lebanon, wanda kuma ya gabatar da Jawabinsa ta kafar Bidiyo daga kasar Lebanon yay aba da yadda manzon Allah (s) yayi mu’amala da nasaran Najran wadanda suka zo masa daga kasar yemen.
Sai kuma Abdolsalam Emami, mai bawa ma’aikatar al-adu shawara kan mabiya mazhabar sunna a nan Iran yayi magana a kan yadda manzon Allah (s) ya zauna da yahudawa a Madina ya kuma kawo misalai da dama wadanda suka shafi hakan.
Sai kuma Amani Mahmoud Ibrahim, sheikhin malami a Jami’ar Al-Azhar ta kasar Masar wanda ya kawo yadda yahudawan Madina suka saba al-kawalin da suka cimma da manzon Allah (s) a farkon hijira da kuma yadda yayi mu’amala da su.