Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu a baya bayan nan suka allawadai da kuma nuna goyon bayansu ga kasar UAE kan mallakar tsibiran Tumb babba da tumb karami da Abu Musa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana cewa bayan duk wani taron da suka gudanar sai kaji cewa wadan nan kasashen Larabawa suna allawadai da Iran kan mallakar wadanan tsibiran, tare da wannan kuma suna kokarin bata dangantaka mai kyau dake tsakanin kasashen yankin da Iran.

Yace yana da tabbaci wasu kasashen duniya ne suke ingiza wadan nan kasashen larabawa su rika tada hankali don a wargaza zaman lafiya da ke tsakanin Iran da kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted