Iran ta sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi sabon shawarwari tsakanin Iran da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: A gobe Juma’a ne za a gudanar da zagaye na biyar na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a birnin Roma.
A lokacin da ya isa birnin Shiraz don halartar taron yankin kan harkokin diflomasiyya na cikin gida, Araghchi ya bayyana cewa, gudanar da wannan taro da ya fi mayar da hankali kan diflomasiyyar tattalin arzikin yankin, ya shiga cikin tsarin manufofin makwabtaka na Iran, yana mai jaddada cewa, ko shakka babu za ta yi tasiri.
Araqchi ya kara da cewa “Za a gudanar da tattaunawar zagaye na biyar ranar Juma’a a Roma babban birnin Italiya.”
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i a cikin wata sanarwa da ya fitar ya yi nuni da shawarar da masarautar Oman ta gabatar da kuma tuntubar da take gudanarwa na gudanar da wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a gobe Juma’a a birnin Roma na kasar Italiya, inda ya sanar da amincewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da wannan shawara.