Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya

Mai bai wa shugaban kasar Iran  shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta

Mai bai wa shugaban kasar Iran  shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa.

Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a yayin taron kasa da kasa na mata da aka bude a kasar China.

Haka nan ta kuma bayyana cewa; A wannan lokacin muna rayuwa ne a cikin karnin da ci gaba da fasahar kere-kere su ka sauya salon rayuwa, ta yadda kirkirarriyar fasaha ta zama mai matukar tasiri a cikin matakan da ake dauka, kamar kuma yadda Sakandami ( Robot) ya maye gurbin bil’adama a cikin wasu fagage.”

Mai bai wa shugaban kasar Iran din shawara akan harkokin mata da iyali ta ci gaba da cewa; Tare da gagarumin ci gaban da ake da shi a fagen kere-kere sai dai kuma bai zama mai hada zukata ba, da hakan ya sa tazara mai yawa ta karu a tsakanin masu shi da marasa shi,kuma mutane suna kara zama cikin kadaici.

Haka nan kuma ta yi ishara da yadda ake kasuwanci da yake-yake da wasa da kwakwalen mutane da yadda kiyayya da gaba a cikin fagagen sadarwa na jama’a.

Zahra Behruz Azar ta ce jin kai da tausayawa su ne abubuwan da za su dawo da ruhin ‘yan’adamtaka a cikin duniyar da tashe-tashen hankula su ka ci dununta.

Dangane da rawar da mata suke takawa a Iran, Malama Zahra Behruz ta ce; Matan da suke cikin jami’oi a Iran sune kaso 60%, yayin da fagen kirkire-kirkire su ka kai kaso 24%. Lokitocin da ake da su a fadin Iran kuwa, mata ne kaso 40%, sai kuma masu bayar da shawar akan harkar kiwon lafiya da sun kai 30%.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments