Iran Ta Fara Fidda Takardun Sirri Tsakanin HKI Da Hukumar IAEA

Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA

Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa yanzu ya nuna irin yadda hukumar IAEA take mika bayanan da ta samu daga cibiyoyin Nukliya na kasar Iran ga HKI. Wanda ya kaiga kissan masana da kwararrun a fasahar makamacin Nukliya a baya.

Bayanan sun bayyana yadda hukumar ta IAEA take mikawa dukkan takardun sirri na shirin makamashin nukliya na kasar Iran ga makiyanta don su yi aiki a kai.

Banda HKI wadannan bayanan sun isa hannun hukumomi a kasashen yamma musamman Amurka.

Sannan sun tabbatar da cewa hukumar IAEA bata yin adalci a cikin ayyukanta. Amma daraktan hukumar Rafael Grossi ya bayyana cewa abinda gwamnatin Iran take fada dangane da shi da kuma hukumarsa ba gaskiya bane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments