Iran Ta Cilla Tauraron Dan’adam Mai Suna Nahid-2 A Yau

JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar

JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya. Banda tauraron dan’adam na kasar Iran ita ma kasar Rasha tana da taurarin dana dam guda biyu a cikin kumbon wato Ionosfera-M3 da M4, sannan da wasu 18 na wasu kasashe.

Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika taurarin dan’adam na kasar Iran guda 3 wato Khayyam, Parsa -1 da kuma hudhod.

Manufar cilla Nahid -2 dai shi ne kyautata harkokin sadarwa na JMI a sararin samaniya. Kuma kamfanonin gina taurarin yan adama a cikin kasa ne suka hada kai don ganin ya kammala.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments