Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’ie ya bayyana korar da gwamnatin kasar Australia ta yiwa Jakadan kasar daga bienin Camberra saboda abinda ta kira kin yahudawa, ta raba ne da wannan zargin don ta bayyarta da JMI. Ya kuma sha alwashin cewa Iran zata rama.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Bakhaee yana fadar haka a yau talata, ya kuma kara da cewa, idan ana maganar ‘kin yahudawa’ ko “anti-Semitism,” Ai kasashen turai ne asalin wannan halin ta kin wata kabila, kuma tarihi ta tabbatar da cewa a Turai ne aka fara “anti-Semitism,” kan yahudawa a yakin duniya na biyu. Turawa ne suka fara kin Yahudawa a duniya suka kuma kashesu. Amma kasar Iran bata da wannan mummuna halin a tarihin kasar sai ma sabanin haka, Iraniyawa sun taba kubutar da yahudawa daga bauta.
Amma iran ba bu kin wata kabila a cikin addininsu, ko aladunsu ko wani abu mai kama da haka. Kafin haka dai a yau talata ce firai ministan kasar Autralia Anthony Albanese, ya bada sanarwan korar Jakadan kasar Iran a birnin Camberra saboda abinda ya kira ‘Kin yahudawa’ ko Anti-semetism’. Bakha e= yake Iran zata rama, kuma matakin da kasar Autra lia ta dauka ya bayyana yadda Australia take kin JMI, sannan tana ganin yin haka zai canza ra’ayin mutanen Australia wadanda suka fito kwansu da kwarkwatansu suna allawadai da HKI kan kissan da take yi a Gaza.