Iran Ta Ce Rashin Kawar Da Tushen ‘Yan Ta’adda A Siriya Zai Mayar Da Kasar Tushen Ta’addanci

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rashin kawar da tushen ta’addanci daga Siriya zai mayar da kasar sansanin kungiyoyin ‘yan ta’adda Ministan harkokin

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rashin kawar da tushen ta’addanci daga Siriya zai mayar da kasar sansanin kungiyoyin ‘yan ta’adda

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Rashin nuna sha’awar kasashen yankin wajen yakar ta’addanci da kawar da tushensa a kasar Siriya, zai sanya kasar ta zama sansani da kuma daukar nauyin yaduwar kungiyoyin ‘yan ta’adda a duk fadin yankin.

A ganawarsa da fira ministan kasar Iraki Muhammad Shi’a al-Sudani a yau Juma’a: Abbas Araqchi a ziyarar da kai birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki ya jaddada cewa: Goyon bayan dukkan kasashen yankin ga Siriya da Iraki ya zama wajibi, kuma yana da matukar muhimmanci wajen yaki da kuma kokarin murkushe ‘yan ta’adda.

Haka nan ya kuma yi ishara da kokarin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi na ci gaba da tuntubar juna a tsakanin kasashen biyu bisa la’akari da halin da ake ciki a halin yanzu, inda ya ce: Gwamnatin Iraki da al’ummar kasar suna dauke da mummunar tunani dangane da yaduwar wannan lamari na ta’addanci, kuma duniya ta ga irin gagarumin kokari da sadaukarwa da al’umma da gwamnati da kuma cibiyoyin Iraki suka yi, don shawo kan wannan mawuyacin hali da kuma murkushe ta’addanci da suka yi a kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments