Iran Ta Ce Gabatar Da Bukatar Dakatar Da Tashe Makamashin Uranium Karshen Tattaunawar Da Amurka

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Rvanchi ya bayyana cewa a duk lokacinda gwamnatin Amurka ta gabatar da dakatar da tache makamacin Uranium

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Rvanchi ya bayyana cewa a duk lokacinda gwamnatin Amurka ta gabatar da dakatar da tache makamacin Uranium a cikin Iran tattaunawar ba zata je ko in aba.

Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Steve Wit-koff jakadan shugaba Trump na musamman a yanking abas ta tsakiya, kuma wakilinsa a tattaunawar Tehran da Washingtong kan shirin makamashin Nukliyar Iran ya fadawa kafafen yana labarai kan cewa duk wata yarjeniya da za’a kulla da Iran a kan shirinta na makamashin Nukliya sai ya hada da rashin tashe makamashin Uranium a cikin kasar Iran, wanda zai nesantata daga makaman Nukliya.

A nasa bangaren Takhta Ravanci ya bayyana cewa tun farko Iran ta bayyana cewa batun tace makamashin Uranium a cikin gida alfakharin kasarmu don haka ba ma abinda tattaunawa ne da wata kasa ba.

Sai dai ya kara da cewa, duk tare da cewa Amurka takan bijiro da wasu al-amura ga kafafen yada labarai sabanin abinda take bayyana wa a fagen tattaunawa, Iran zata ci gaba da halattan tarurrukan tattaunawar sai randa Amurka ta gabatar da wannan bukatar ta kuma sake jin ansar da muka sha nanatawa kan cewa batun tashe makamashin Uranium a cikin kasa bayan cikin ajendar Iran da Amurka.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments