Iran Ta Ce Babu Batun Tattaunawa Duk Tare Da Amurkawa Sun Ce Za’a Yi

Kakakin gwamnatin JMI ta bayyana cewa a dai-dai lokacinda Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar , babu wata tattaunawa da Amurka nan

Kakakin gwamnatin JMI ta bayyana cewa a dai-dai lokacinda Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar , babu wata tattaunawa da Amurka nan kusa, duk tare da cewa Amurkawan sun bayyana cewa za’a ci gaba da shi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin gwamnatin kasar Iran Malama Fatimah Muhajirani tana fadar haka a jiya Talata, ta kuma kara da cewa, babu wata rana da aka sanya na tattaunawa da Amurka kuma mai yuwa babu wata tattaunawa da ita nan kusa.

Fatima tana maida martani ne ga wata sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayara na, na cewa nan kusa zasu sake farfado da tattaunawa da JMI.  Tehran dai ta bayyana cewa bata bukatar wani tattaunawa da Amurka kuma bayan hare-haren da ta kai kan cibiyoyin nukliyar kasar guda 3 a dai dai lokacinda HKI ta fadawa kasar da yaki tare da amincewarta.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted