Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan

Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan

Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.

A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.

Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments