Iran Ta Ce Akwai Sauyi Ta Yadda Zata Ci gaba Hulda Da Hukumar IAEA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar IAEA zai sauya saboda hare-haren da HKI ta kaiwa cibiyoyin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar IAEA zai sauya saboda hare-haren da HKI ta kaiwa cibiyoyin makamashi nukliya na kasar iran a cikin watan yunin da ya gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto Baghaei yana fadar haka a yau litinin ya kuma kara da cewa, ma’amalar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta IAEA zai sauya gwagwadon yadda al-amura suka sauya bayan yakin kwanaki 12 da HKI da kuma Amurka.

Ya ce har’ila yau mu’amalar zata kasance bisa rahoton da hukumar ta IAEA ta aikawa iran da kuma wasu abubuwan da shugaban hukumar Rafael groosy ya ke riyawa a cikinsa. Da farko iran zata mayar masu da ansa. Sannan zata gabatar da sabbin sharuddan aiki da hukumar.

Baqae ya ce ‘ mun karanta rahoton kuma zamu maida martani kansa, gareshi ga kuma gwamnoninsa. Ya ce Iran tana tsamman zasu yi mata adalci bayan yakin kwanaki 12, saboda abinda ya shafi cibiyoyin nukliyar kasar. amma hakan bai faru ba.

Ya ce yakamata hukumar IAEA ta gane kan cewa Iran ba zata kuma aikwatar da ka’idojin hukumar kamar yadda yake kafin yakin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted