Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi wannan kiran ne bayan wata maganan da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya yi dangane da kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa, Hakan Fiddan ya bayyana cewa shirye-shiryen JMI a kasar Siriya masu rusa kasar ne, kafin juyin mulkin da Turkiyan ta dauki nauyinsa a baya-bayan nan a kasar Siriya.
Ya ce: Fidan yana magana kan gagarumin taron Jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasaralla wanda aka gudanar a birnin Beirut na kasar Lebanon a ranar Lahadi 23 ga watan Fabrairun da ta gabata. Tare da halattar manya-manyan jami’an gwamnatin kasar.
Baghaei ya ce: Ministan yana nufin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya kai zuwa taron na Jana’iza da ganawar da yayi da Jami’an gwamnatin kasar Lebanon a lokacin, da zuwan sa Geneva inda ya halarci taron kwance damarar makaman Nukliya, da kuma ganawarsa da ministocin harkokin wajen kasashen Indonasia, Bahrain, Kuwait da kuma wasu a gefen taron.
Ya ce Iran tana maganar a dai dogaro da manya-manyan kasashen duniya, kuma kasashen yankin su magance matsalolinsu da kansu.