Search
Close this search box.

Iran Ta Bukaci Taron Gaggawa Na Kwamitin Sulhu Bayan Kisan Nasrallah

Iran ta bukaci taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan kisan shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah a harin da Isra’ila ta kai,

Iran ta bukaci taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan kisan shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah a harin da Isra’ila ta kai, ta hanyar amfani da bama-bamai a kudancin Beirut..

A cikin wata wasika, jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Saeid Iravani ya yi kira ga majalisar da ta dauki matakin gaggawa don dakatar da kai hare-haren Isra’ila tare da hana jefa yankin cikin yakin basasa.

A cikin wasikar da ya aike wa shugaban majalisar, Iravani ya bukaci mambobin kungiyar mai wakilai 15 da su yi Allah wadai da kakkausar murya akan “ayyukan ta’addanci” na Isra’ila.

Iravani ya kuma yi gargadin ‘’Mai karfi” game da “duk wani hari kan wuraren diflomasiyya da wakilai na Iran”.

Isra’ila, dai na ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a Lebanon, inda ko a wannan Asabar mutane 33 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila tare da jikkata wasu 195, a cewar ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce, hare-haren da Isra’ila ta kai kan yankunan Lebanon ya yi sanadin mutuwar mutane 33 ranar Asabar tare da raunata mutane 195, a rana ta shida na hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke ikirarin ka iwa kan maboyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments