Iran Ta Bukaci Musulmi Su Hada Kai Da Siriya Wajen Fatattakar ‘Yan ta’adda

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya yi kira ga kasashen musulmi da su hada kai tare don taimakawa kasar Siriya wajen fatattakar kungiyoyin ‘yan ta’adda

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya yi kira ga kasashen musulmi da su hada kai tare don taimakawa kasar Siriya wajen fatattakar kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke barazana ga kasar ta Larabawa.

Shugaba Pezeshkian ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Iraki Mohammed Shia’ Al Sudani.

Mista Pezeshkian ya ce, kare martabar yankunan kasashen yankin da suka hada da Syria na daga cikin manufofin Iran game da yankin.

Iran a shirye take ta ba da hadin kai don tunkarar ayyukan ta’addancin da ake ci gaba da yi a kasar Siriya da nufin kare tsaron yankin, in ji Pezeshkian kafin ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin kasashen musulmi domin taimakawa kasar Siriya wajen fatattakar ‘yan ta’adda.

Ya ce sabbin abubuwan da suke faruwa a Siriya sun haifar da matukar damuwa game da tsaron yankin a daidai lokacin da yankin ke son komawa cikin kwanciyar hankali bayan tsagaita bude wuta da aka yi a Labanon, kuma aka zura idanu zuwa ga Gaza.

Shugaba Pezeshkian ya yi gargadin cewa: “Irin wadannan abubuwa wani bangare ne na mununan makircin gwamnatin sahyoniyawan don yada rikici da tashin hankali a kasashen musulmi,” inda ya yi kira da a yi kokarin hadin gwiwa da kasashen musulmi don hana yaduwar irin wadannan ayyukan.

A nasa bangaren, firaministan kasar Irakin ya ce ayyukan ta’addanci na baya-bayan nan a kasar Siriya wani yunkuri ne na gwamnatin Isra’ila na gurgunta tsaro da ‘yancin kai da kuma yankin kasar ta Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments