Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi kira ga kasashen yankin Asiya ta kudu da su hada kai. Su kuma samar da runduna wacce zata tunkari HKI a kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka, a shafinsa na X a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa sojojin HKI sun lalata kusan dukkan kayakin tsaro na kasar Siriya. Banda haka sun kuma lalata hatta wasu wuraren da basu da dangantaka da harkokin tsaro.
Aragchi ya bayyana cewa mamayar karin yankuna na kasar Siriya wanda sojojin HKI suka yi kuma suke kara yi, a kasar Siriya ya sabawa kudurin MDD ta shekara 1974, wacce ake kira UNSCR 351.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ce, kadangaren bakin tulun da ta hana samun zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu. Yace kwamitin tsaro na MDD wanda yakamata ya zama hukuma mai tabbatar da zaman lafiya a duniya, ya zama majarradin mai sanya ido ko kuma mai yin allawadai da duk abinda Amurka da HKI suka yi wadanda ba dai-dai ba.
Ministan ya kammala da cewa, kasashen da suke makobtaka da kasar Syriya yakamata su taimaka mata.
Daga karshe yayi kira ga dukkan kasashen larabawa da musulmi da kuma dukkan mambobin MDD su tabbatar da cewa an bi dokokin kasa da kasa. Don rashin aiki da su zai maida duniyar kamar rayuwar daji.