Iran Ta Bukaci Hadin Kan Kasashen Yankin Don Dakile Ayyukan Isra’ila A Siriya

Ministan harkokin wajen Iran ya yi kira ga kasashen yankin da su hada karfi da karfe domin dakile anniyar gwamnatin Isra’ila kan kasar Siriya. Abbas

Ministan harkokin wajen Iran ya yi kira ga kasashen yankin da su hada karfi da karfe domin dakile anniyar gwamnatin Isra’ila kan kasar Siriya.

Abbas Araghchi ya fada a cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na X cewa gwamnatin Isra’ila na yunkurin lalata kusan duk wani abu da ya shafi tsaro da kuma kayayyakin more rayuwa a Siriya.

Araghchi ya kara da cewa gwamnatin kasar ta kuma mamaye wasu yankuna na Syria wanda ya sabawa yarjejeniyar shekarar 1974.

Ministan harkokin wajen Iran Ya kuma bayyana Amurka a matsayin babban abin da ke kawo cikas ga dakatar da tashe-tashen hankula a yankin.

Ya kuma yi kira ga kasashen da ke makwabtaka da Syria da sauran kasashe su maida anniya kan kasar ta Siriya.

Bai kamata “Makwabtan Siriya, da na larabawa da na musulmi da kuma duk wata kasa memba ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da bin doka da oda, su nuna halin ko in kula ba.” Game da lamarin Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments