Rahotanni sun bayyana cewa majalisar shawarar musulunci ta kasar iran ta sanar da amincewa da Mehrdad Akhlaqhi a matsayin sabon ministan tsaron kasar da kuma shugaban kula da muhimmman kayayyakin soji, bayan da yan majalisar suka kada kuri’ar da mafi rinjaye na amincewa da shi.
Majalisar ta yi bitar takardu da shirye shiryensa a lokacin zaman da aka yi a wanda kakakin majalisa mohammad Baqeer Qalibaf ya jagoranta kafin a fara kada kuri’a. inda ya samu kuri’u 237 ta nuna amincewa yayin da kuma guda 15 na nuna rashin amincewa, kuma babu wanda ya janye daga cikin yan majalisar 277 , da hakan ya bashi damar amincewa da shi a matsayin sabon ministan tsaro
Shugaban kasar iran mas’ud pezeshkiyan ya gabatar da sunan akhlaghi ne a matsayin sabon ministan tsaro a ranar 5 ga watan oktoba domin neman amincewar kwararrun majalisar
Shugaban kasar Iran mas’ud pezeshkiyan yayi bayani ga yan majalisa domin nuna goyon bayan wanda aka zaba, yayin da yan majalisar da suka nuna adawa ko goyon baya ga tsare-tsarensa suka gabatar da raayoyinsu kafin daga bisani Akhlaghi ya kare shirin da ya gabatar