Ministan harkokin harkokin wajen kasashen Iran da Rasha sun gudanar da tattaunawa ta wayar tarho dangane da halin da ake ciki nay akin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan kasar ta Iran, da kuma yadda suka haifar da matsaloli a yankin da sua shafi duniya duniya baki daya.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, manyan kasashe masu tasiri a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya irin su Rasha da China da sauran kasashe, bai kamata su bar Amurka tana wasa da kwamitin yadda ta g dama ba.
Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Rasha Segey Lavrov ya bayyana cewa, harin Amurka da Isra’ila a kan Iran ya sabawa dukaknin dokokin duniya, kuma dole ne a kawo karshensa ba tare da wani bata lokaci ba.