Iran Na Shirin Cilla Tauraron Dan’adam Da Sandarerren Makamashi A Cibiyar Chabahar

Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren

Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi.

Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu.

Salarieh y ace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran  cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin yan’adam mai amfani da makamashin ruwa.

Kamfanonin taurarin yan’adam na kasar Iran dai suna samar da taurarin yan’adam don ayyukan daban-daban, daga ciki har da sadarwa da kuma ayyukan noma da kula da yanayi da sauransu.

Banda haka hukumar tansa gina taurarin yan’adam haka ma kamfanoni masu zaman kansu a cikin gida, ba tare da taimakon wani daga waje ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted